Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAdam A Zango ya saki sabuwar matarsa Maimuna Musa

Adam A Zango ya saki sabuwar matarsa Maimuna Musa

Rahotanni sun nuna cewa fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya rabu da matarsa, tsohuwar jaruma Maimuna Musa.

Jarumi Ali Rabi’u Ali (Daddy) ya shaida wa Iconic FM Najeriya cewa Maimuna da kanta ta tabbatar masa da rabuwar auren, tare da bayyana cewa tana kan hanyarta ta komawa Kano.

Ali Rabi’u Ali ya kuma bayyana fatan Allah Ya shiga lamarin, Ya kawo zaman lafiya da alheri ga ɓangarorin biyu.

A baya dai an taɓa yin ce-ce-ku-ce kan rayuwar auren Adam A. Zango, inda ake yawan alakanta shi da yawan rabuwa da matan da ya aura.

Sai dai har zuwa yanzu, babu wata sanarwa kai tsaye daga Adam A. Zango da ke ƙarin bayani kan rahotannin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments