Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiGwamnatin tarayya za ta cire tallafin wutar lantarki

Gwamnatin tarayya za ta cire tallafin wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na cire tallafin wutar lantarki daga shekarar 2027, a wani yunƙuri na aiwatar da sauye-sauye masu dorewa a fannin samar da wutar lantarki a ƙasar.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin warware basussukan da suka dabaibaye fannin wutar lantarki, tare da samar da wani tsari da zai hana sake taruwar irin waɗannan basussuka a nan gaba.

A cewarsa, gwamnati za ta dakatar da tallafin daga shekarar 2027, amma ya jaddada cewa matakin ba yana nufin hana ’yan Najeriya cin gajiyar ingantacciyar wutar lantarki ba, sai dai samar da tsarin da zai tabbatar da dorewar ayyukan bangaren.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin rage tarin basussukan da ake bin fannin wutar lantarki da kuma inganta yadda ake gudanar da harkokin samar da wutar lantarki a ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments