Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da ke bai wa matasa damar samun ilimi, ƙwarewa da ayyukan yi domin rage matsalolin tsaro da bunƙasa ci gaban ƙasa.
Ya bayyana hakan ne yayin taron tsaro na Yankin Kudu maso Gabas na shekarar 2026 da aka gudanar a Umuahia, Jihar Abia, inda ya jaddada cewa zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙan haɗin kan ƙasa da bunƙasar tattalin arziki.
A cewarsa, samar da tsaro mai ɗorewa ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, sai an haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro, gwamnatoci, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, ƙungiyoyin farar hula da sauran al’umma.
Mohammed Idris ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu na ƙarfafa hukumomin tsaro ta hanyar inganta musayar bayanan sirri, samar da kayan aiki na zamani, horas da jami’ai da kuma faɗaɗa haɗin gwiwa da ƙasashen duniya.
Ministan ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su guji yaɗa labaran ƙarya, su ci gaba da ba hukumomin tsaro haɗin kai, tare da goyon bayan sauye-sauyen da za su ƙarfafa tsarin tsaro a faɗin ƙasar.