Monday, October 19, 2026
HomeSiyasaTinubu ga ’yan adawa: Ku shirya fafatawa a 2027, ba zan ja...

Tinubu ga ’yan adawa: Ku shirya fafatawa a 2027, ba zan ja da baya ba

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba zai yi sassauci ga masu neman kwace mulki daga hannunsa a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 ba, yana mai cewa siyasa gasa ce da kowa ke da damar shiga, kuma za a fafata har zuwa ƙarshe.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi tawagar Ƙungiyar Bishof-Bishof na Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ya ce ba zai ba wa abokan hamayyarsa damar da za su yi amfani da ita wajen kayar da shi ba.

Ya kuma kare Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa tana gudanar da ayyukanta cikin adalci kuma ba ta nuna son kai ko tsoratar da kowace jam’iyyar siyasa.

Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta aiwatar cikin shekaru uku sun fara haifar da sakamako mai kyau, yana mai bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su amfani ’yan Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments