Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiShaye-shaye na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa laifuka a Kano...

Shaye-shaye na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa laifuka a Kano – Muhyi Magaji

Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin-Gado, ya bayyana cewa kusan kashi 70 cikin 100 na manyan laifukan da ake aikatawa a jihar na da alaƙa da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Ya ce matsalar shaye-shaye na ci gaba da haddasa aikata laifuka kamar fashi, tashin hankali, kisan kai da sauran ayyukan da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron al’umma.

Muhyi Magaji ya jaddada buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, iyaye, malamai da al’umma wajen yaƙi da matsalar, yana mai cewa magance shaye-shaye na da matuƙar muhimmanci wajen rage yawaitar laifuka a Kano.

Ya kuma yi kira ga matasa da su guji amfani da miyagun ƙwayoyi tare da rungumar ilimi, sana’o’i da ayyukan da za su amfani kansu da al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments