Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto mutane 48 da aka yi garkuwa da su bayan sun fatattaki harin ’yan bindiga a ƙauyen Magami da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, bayan sojoji sun samu kiran gaggawa cewa wasu ’yan ta’adda ɗauke da makamai, waɗanda ke haye a babura kusan 40, sun mamaye ƙauyen tare da yin garkuwa da wasu mazauna yankin.
Jami’in yaɗa labarai na Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce ’yan bindigar sun tattara mutanen tare da shirin tafiya da su cikin daji, yayin da wasu daga cikinsu suka tsaya a wajen ƙauyen tare da baburansu.
Ya ce sojojin sun isa wurin cikin gaggawa tare da fafatawa da ’yan ta’addan da musayar wuta mai tsanani, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa dajin da ke kusa, inda suka bar dukkan mutanen da suka yi garkuwa da su.
A yayin harin, mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu biyu suka samu raunukan harbin bindiga. An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Kaura Namoda domin samun kulawa.
Bayan ceto mutanen, sojojin sun gudanar da sintiri mai ƙarfi a yankin da kewaye domin hana sake kai hare-hare. Rundunar ta kuma yaba wa sojojin bisa jarumtaka da ƙwarewarsu, tare da kira ga mazauna yankin da su ci gaba da ba jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.