Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTsayar da ɗan takarar gwamna a Kano a APC zai haifar da...

Tsayar da ɗan takarar gwamna a Kano a APC zai haifar da rarrabuwar kai — Ganduje

Tsohon gwamnan jihar Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya, kuma jagoran jam'iyyar APC, ya gargadi masu fitowa suna ayyana wani mutum a jam'iyyar da cewa shi aka amince ya yi takarar gwamnan jihar a babban zaben 2027.

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce har yanzu lokaci bai yi ba da wasu za su rika fitowa suna cewa ga wanda zai yi takara ba saboda a cewarsa hakan zai sake haifar da rarrabuwar kai a jam’iyyarsu ta APC.

Tun da fari dai wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC ne a Kano suka amince da cewa sanata Barau Jibrin, shi ne zai yi takarar gwamna a jihar a 2027.

Ga alama dai wannan dambarwa ta ayyana sanata Barau Jibrin, a matsayin wanda wa su ke so ya yi wa jam’iyyar APC takarar gwamnan jihar na ci gaba da daukar hankali, musamman bayan da Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya takawa maso fitowa suna nuna goyon baya ga wani mutum daya birki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments