Ƙungiyar Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta sake tabbatar da aniyarta na ƙaddamar da kuɗin bai ɗaya na yankin, ECO, a shekarar 2027 domin ƙarfafa haɗin kan tattalin arziki da bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashen yankin.
An bayyana hakan ne bayan taron shugabannin ƙasashen ECOWAS karo na 69 da aka gudanar a birnin Lungi na ƙasar Saliyo, inda shugabanni suka ce ECO zai kasance wani muhimmin mataki wajen ƙarfafa haɗin gwiwar tattalin arziki da samar da ci gaba mai ɗorewa.
Sai dai ECOWAS ta bayyana cewa ba dukkan ƙasashe za su fara amfani da kuɗin lokaci guda ba, domin ƙasashen da suka cika sharuɗɗan tattalin arzikin da aka gindaya ne za su fara amfani da shi, yayin da sauran za su ci gaba da samun tallafi har sai sun cancanta.
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan matsalolin tsaro da ke addabar yankin Sahel da kuma yawaitar garkuwa da mutane, musamman a Arewacin Najeriya, tana mai jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa wajen magance matsalolin tsaro da bunƙasa ci gaban yankin.