Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe mutum biyu, sun jikkata wasu uku tare da yin garkuwa da mutum biyar a wani sabon hari da suka kai ƙauyen Kwaren Gamba da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto. Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 12:45 na dare ranar Asabar, inda suka ba mazauna yankin mamaki, lamarin da ya sa mutane da dama suka tsere domin tsira da rayukansu.
Mutanen da suka rasa rayukansu sun haɗa da Nasiru Ibrahim, wanda aka fi sani da Nasiru Dan Tanin, da kuma Mansir Sani. Haka kuma, Halilu Mai Shago, Hamisu Dan Musa da Abdulwahab Salihu (Jari) sun samu raunuka, kuma a halin yanzu suna karɓar magani a wani asibiti. Mazauna yankin sun ce waɗanda aka sace sun haɗa da Saifullahi Saminu, Abdullahi Salihu Dogo da wasu mata uku.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Daily Trust cewa ba su samu wata sanarwa ko bayanan sirri kan zuwan maharan ba kafin harin. Ya ce lokacin da ’yan bindigar suka shiga ƙauyen, kowa ya nemi mafaka saboda babu lokacin da za su shirya wata kariya ko turjiya.
Ya ƙara da cewa wannan sabon hari ya zo ne kwanaki biyar kacal bayan da ’yan bindiga suka kai wani farmaki a wannan ƙauye, inda suka sace mata biyar da wani jariri. A cewarsa, a wancan lokacin ’yan sa-kai da wasu mazauna yankin sun bi sawun maharan har wajen ƙauyen, amma duk da haka sun tsere tare da mutanen da suka yi garkuwa da su.
A wani lamari makamancin haka a ƙauyen Makuwana, wanda shi ma ke ƙaramar hukumar Sabon Birni, wani mazaunin yankin ya ce ’yan bindiga sun kai hari tun ranar 23 ga Yuni, inda suka sace fiye da mutum 14. Ya ce daga baya sun sako ɗaya daga cikin waɗanda suka sace domin ya isar da saƙon cewa za su sake dawowa su kai wani hari. A daren Asabar sun dawo kamar yadda suka yi barazana, amma ba su samu damar sace kowa ba, sai dai sun kwashe dabbobin wasu mazauna yankin.
Mazauna ƙauyukan Kwaren Gamba, Makuwana da sauran yankunan Sabon Birni sun roƙi gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Sokoto da su tura ƙarin jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyinsu. Sun ce hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da ƙaruwa, duk da cewa yankunan na fama da ƙarancin jami’an tsaro. Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, bai yi nasara ba domin bai amsa kira ko saƙonnin da aka aika masa ba har zuwa lokacin kammala rahoton.