Ƙungiyar kare haƙƙin jama’a ta SERAP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja tana neman umarnin da zai tilasta wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta binciki wasu zarge-zargen da ake yi kan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen 2027.
SERAP ta ce ana zargin wasu gwamnonin jam’iyyar APC da karkatar da kimanin Naira biliyan 800 daga kuɗaɗen rabon tarayya (FAAC), inda ake zargin suna tura gudummawar wata-wata daga baitul malin jihohinsu zuwa wani asusun da ake amfani da shi wajen shirye-shiryen zaɓen 2027.
A cikin ƙarar, ƙungiyar ta bayyana cewa idan ba a binciki waɗannan zarge-zargen ba, hakan na iya jefa sahihanci da adalcin tsarin zaɓe cikin matsala, tare da rage amincewar jama’a da yadda ake gudanar da harkokin dimokuraɗiyya.
SERAP ta kuma buƙaci kotu ta umarci INEC da ta bayyana sahihin tushen kuɗaɗen da ake amfani da su wajen yaƙin neman zaɓe, tare da tabbatar da cewa dukkan jam’iyyun siyasa suna bin tanade-tanaden dokar zaɓe game da tara da kashe kuɗaɗen kamfe.