Jam’iyyar ADC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ceto mutanen da har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Jam’iyyar ta bayyana cewa nasarar da aka samu wajen ceto ɗaliban da malamansu da aka sace a jihar Oyo ya nuna cewa idan aka haɗa kai tare da ingantattun bayanan sirri, ana iya ceto waɗanda ke tsare a hannun ’yan bindiga.
A cewar ADC, ya zama wajibi hukumomin tsaro su mayar da irin wannan ƙwazo kan sauran jihohin da ke fama da matsalar satar mutane, domin tabbatar da cewa duk waɗanda aka yi garkuwa da su sun samu ’yanci cikin gaggawa.
Jam’iyyar ta kuma buƙaci a ƙara inganta tattara bayanan sirri, da faɗaɗa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, tare da gano maboyar masu garkuwa da mutane domin ceto waɗanda suke tsare da kuma daƙile ayyukan ta’addanci.