Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiOnanuga ya caccaki Atiku kan rashin yin tsokaci bayan ceto ɗaliban Oyo

Onanuga ya caccaki Atiku kan rashin yin tsokaci bayan ceto ɗaliban Oyo

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya soki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, kan rashin mayar da martani bayan jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo.

A cewar Onanuga, Atiku ya kasance mai yawan sukar gwamnatin tarayya a lokacin da waɗanda aka sace ke hannun masu garkuwa da mutane, amma ya ce har bayan sa’o’i 18 da samun nasarar cetonsu bai fitar da wata sanarwa ko yin tsokaci kan lamarin ba.

Ya kuma yaba da matakin da Peter Obi ya ɗauka na maraba da nasarar aikin ceton tare da gode wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu, duk da cewa bai yi yabon Shugaba Bola Ahmed Tinubu kai tsaye ba.

Onanuga ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu nasarar ceto ɗaliban da malamansu ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Ya ƙara da cewa an kama mutum takwas da ake zargi da hannu wajen sace su, yayin da wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen suka mutu a yayin gudanar da aikin ceton.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments