Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da bai wa ma’aikatan gwamnati mata hutun haihuwa na tsawon watanni shida domin ba su damar shayar da jariransu yadda ya kamata.
Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Ma’aikatan Jihar, Yakubu Haidara, ne ya sanar da wannan mataki a Gusau yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar farar hula ta (CS-SUNN).
A cewarsa, manufar wannan mataki ita ce inganta lafiyar uwa da jariri tare da ƙarfafa shayar da jarirai nono zalla a watanni shida na farko, kamar yadda masana lafiya ke ba da shawara.
An yi maraba da wannan mataki, inda ake ganin zai taimaka wajen bunƙasa walwala da lafiyar iyalai, tare da ƙarfafa jin daɗin ma’aikatan gwamnati mata a jihar Zamfara.