Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Benuwe ta rusa sama da shingayen bincike 20 da aka kafa...

Gwamnatin Benuwe ta rusa sama da shingayen bincike 20 da aka kafa ba bisa ƙa’ida ba

Gwamnatin Jihar Benuwe ta rusa sama da shingayen bincike 20 da aka kafa ba bisa ƙa’ida ba a kan hanyar Vandeikiya–Konshisha, domin dakile karɓar kuɗin haram da sauƙaƙa zirga-zirga.

Gwamnatin Jihar Benuwe ta rusa sama da shingayen bincike 20 da aka kafa ba bisa ƙa’ida ba a kan hanyar Vandeikiya–Konshisha, domin dakile karɓar kuɗin haram da sauƙaƙa zirga-zirga.

Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin tsaro da cikin gida, Joseph Har, ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa daga cikin sama da shingaye 20 da ke kan hanyar, uku ne kawai suka kasance na hukuma, yayin da sauran wasu matasa da masu ikirarin jami’an gwamnati ke amfani da su wajen karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakai kan duk wanda aka samu da laifin kafa irin waɗannan shingaye, tare da ƙarfafa al’umma su riƙa kai rahoton duk wani aikin karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba ga hukumomin tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments