Monday, October 19, 2026
HomeKasashen wajeSabon fada ya ɓarke tsakanin Pakistan da Afghanistan

Sabon fada ya ɓarke tsakanin Pakistan da Afghanistan

Faɗan kan iyaka ya sake ɓarkewa tsakanin dakarun Pakistan da na gwamnatin Taliban ta Afghanistan, inda kowane ɓangare ke zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wuta

Mazauna garin Spin Boldak na Afghanistan sun tsere daga gidajensu, wanda ke kan iyakar ƙasashen mai tsawon kilomita 2,600.

Wani ma’aikacin lafiya a garin Kandahar ya bayyana cewa an kai gawar mutum huɗu asibitin yankin tare da raunata wasu mutum huɗu.

An kuma raunata wasu mutum uku a Pakistan.

Ƙasashen biyu dai sun yi ta gwabzawa a ‘yan watannin nan, yayin da Taliban ke zargin Pakistan da kai hare-hare ta sama cikin Afghanistan.

Ɓangarorin biyu sun tabbatar da fafatwar a cikin dare amma sun zargi juna da fara kai harin da ya jawo ɓarin wuta na kusan awa huɗu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments