Wata kotu mai hukunta masu karya dokokin ɗabi’a a Iran ta yanke wa fitacciyar mawaƙiyar ƙasar, Parastoo Ahmadi, hukuncin bulala 74 bayan ta gabatar da wani shirin raye-raye ta shafin YouTube ba tare da sanya hijabi ba.
Baya ga hukuncin bulala, kotun ta kuma haramta mata fita daga Iran na tsawon shekaru biyu, tare da dakatar da ita daga gudanar da harkokin waƙa da kiɗa na wani ɗan lokaci.
Rahotanni sun ce hukuncin ya biyo bayan zargin cewa ta karya dokokin ƙasar da suka wajabta wa mata sanya hijabi a bainar jama’a da kuma yayin gabatar da shirye-shirye.
Hukuncin ya haifar da martani daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam, waɗanda suka yi Allah wadai da matakin, suna mai cewa yana ƙara nuna tsauraran dokokin da ake aiwatarwa kan mata da kuma tauye musu ‘yancin faɗar albarkacin baki da bayyana ra’ayinsu a Iran.