Wasu ’yan bindiga da ke addabar yankunan Jihar Zamfara sun yi garkuwa da mutane da dama, mafi yawansu dattijai, bayan sun gayyace su zuwa wata ganawa da aka shirya domin tattauna yiwuwar cimma yarjejeniyar zaman lafiya.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani daji da ke kusa da Magamin Diddi a Ƙaramar Hukumar Maradun, inda mutanen suka je domin halartar zaman da aka ce zai taimaka wajen rage rikici tsakanin al’umma da ’yan bindigar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa akalla mutum 39 aka kama a ranar Lahadi yayin taron.
Sai dai wasu mazauna yankin da jami’an tsaro sun ce adadin waɗanda aka yi garkuwa da su na iya kaiwa kusan mutum 50.
A cewar rundunar, mahalartan taron suna tattaunawa ne da wasu da ake zargin suna da alaƙa da shugaban wata ƙungiyar ‘yan bindiga domin neman mafita ga matsalolin tsaro da kuma sassauta ƙuntatawar zirga-zirga da ke shafar al’ummomin yankin.
Jihar Zamfara dai na daga cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren ‘yan bindiga a Najeriya, inda ake yawan samun garkuwa da mutane, kashe-kashe da kuma kai farmaki kan ƙauyuka.
Rikicin ya jawo asarar rayuka, raba dubban mutane da muhallansu tare da kawo cikas ga ayyukan noma da tattalin arzikin al’umma.