Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTrump ya juya wa Netanyahu baya kan yakin Iran

Trump ya juya wa Netanyahu baya kan yakin Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan duk wani sabon matakin yaƙi da Isra’ila za ta ɗauka kan Iran ba, yayin da rikicin da ya daɗe yana ci gaba tsakanin ƙasashen biyu ke fuskantar wani sabon salo.

Rahotanni sun nuna cewa Trump ya isar da wannan saƙo ne ga Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da suka yi a ranar Litinin.

Gargadin na zuwa ne a daidai lokacin da Iran da Isra’ila suka amince da dakatar da hare-hare tare da ba da dama ga ci gaba da tattaunawar sulhu domin rage zaman ɗar-ɗar da ke tsakaninsu.

An ruwaito cewa shugaban Amurkan ya shaida wa Netanyahu cewa Isra’ila za ta iya ci gaba da yaki ita kaɗai idan ta zaɓi sake komawa yaƙi da Iran, yana mai jaddada muhimmancin warware rikicin ta hanyar tattaunawa maimakon amfani da ƙarfin soja.

Trump ya kuma yi kira ga bangarorin biyu su ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta tare da kauce wa duk wani mataki da zai iya tayar da sabon rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun kuma nuna cewa akwai ci gaba a tattaunawar da ake gudanarwa a bayan fage domin samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin, yayin da ƙasashen duniya ke ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments