Mahukuntan kasar Spain sun sanar da soke wasan sada zumunci da aka shirya tsakaninta da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, sakamakon bullar cutar Ebola a kasar ta Afirka ta Tsakiya.
Magajin garin La Linea de la Concepcion, Juan Franco, ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin kare lafiyar jama’a da kuma dakile yiwuwar yaduwar cutar zuwa yankin.
Haka kuma, jami’an lafiya sun goyi bayan dakatar da wasan, suna mai gargadin cewa ci gaba da shirya wasan na iya haifar da barazana ga lafiyar al’umma.
A gefe guda, tawagar Congo za ta fafata da Denmark a Belgium, yayin da aka dakatar da atisayensu a gida domin kare ‘yan wasan daga kamuwa da Ebola.
A halin yanzu dai yan wasan suna gudanar da atisayensu ne a Belgium.