Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiWani mutum ya hallaka ɗan uwansa da matarsa a jihar Kebbi

Wani mutum ya hallaka ɗan uwansa da matarsa a jihar Kebbi

Rundunar ‘yan sanda ta kama wani matashi mai suna Idrisu Musa mai shekaru 25, bisa zargin kashe ɗan uwansa, Muhammed Haruna, tare da matarsa Habiba a ƙauyen Asarara da ke yankin Kimba a ƙaramar hukumar Jega ta jihar Kebbi State.

A cewar sanarwar ‘yan sanda, wanda ake zargin ya kai wa ma’auratan hari da adda bayan ya sha yi musu barazana a lokuta daban-daban kafin aukuwar lamarin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar M. Hadejia, ya bayar da umarnin miƙa lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na jihar, SCID domin ci gaba da bincike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments