Gwamnatin Jihar Kano ta amince da rage awannin aikin ma’aikatan gwamnati domin bai wa Watan Azumin Ramadan na 1447AH (2026) muhimmancin da ya dace.
Wannan na kunshe a cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan wata 18 ga Fabrairu, 2026, da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jiha ya fitar, kuma daraktar gudanarwa, Safiyya Suleiman, ta sanya wa hannu a madadin Shugaban Ma’aikatan Jiha.
Takardar, mai lamba HCS/LEV/2/V.II/177 kuma mai taken “Circular No. 2/2026,” ta bayyana cewa ma’aikatan gwamnati za su riƙa yin aiki da rage sa’a ɗaya a kowace rana a tsawon watan azumi.
“Gwamnatin Jihar Kano ta amince da rage sa’a ɗaya na awannin aikin hukuma ga ma’aikata a lokacin azumin Ramadan na 1447AH,” in ji takardar.
An aike da umarnin zuwa manyan jami’an gwamnati da cibiyoyi daban-daban, daga ciki har da Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnati, Sakataren Gwamnatin Jiha, kwamishinoni, Manyan sakatarori, shugabannin sassan da ba na ma’aikatu ba, manyan magatakardun Babbar Kotun Jiha da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a, da kuma shugabannin hukumomi, kwamitoci da kamfanonin gwamnati.
A ƙarƙashin sabon tsarin, daga Litinin zuwa Alhamis za a riƙa aiki daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na rana, ma’ana an rage sa’a ɗaya daga tsarin da aka saba. Sai dai ranar Juma’a za ta ci gaba da kasancewa daga 8:00 na safe zuwa 1:00 na rana kamar yadda aka saba.
Takardar ta ce an yi wannan gyara ne bisa al’adar ba wa watan Ramadan muhimmanci na musamman.
“Wannan mataki ya yi daidai da al’adar ba wa Watan Azumi na Ramadan kulawa ta musamman, tare da bai wa ma’aikata damar gudanar da ibadunsu yadda ya kamata,” in ji sanarwar.
Shugaban Ma’aikatan Jiha ya kuma bayyana fatan cewa za a yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.