Najeriya ta gargadi ‘yan ƙasarta a kan shiga yake-yake a wasu kasashen bayan wani rahoto da ya fito da ke cewa an yaudari wasu ‘yan kasar inda suka shiga yakin da Rasha ta ke yi a Ukraine.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta bayyana matukar damuwarta a kan yadda ake kara samun ‘yan Najeriya da ake dauka aiki ba bisa ka’ida ba domin su je su yi yaƙi a wasu kasashen.
Rahoton dai wanda aka wallafa a makon da ya gabata wanda wasu masu bincike suka gudanar kan sojojin haya na Rasha, ya ce rundunar sojin Rasha ta dauki ‘yan Najerya akalla 36 aiki domin su yi yaki a Ukraine inda aka kashe mutum biyar daga cikinsu.
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce,”Yawancin ‘yan Najeriyar da aka dauka irin wannan aiki an tura su fagen daga bayan an yaudaresu da cewa za a ba su aiki a rundunar sojin Rasha.”
A makon daya gabata wani bincike da kamfanin dillancin labarai na AFP ya yi ya gano wasu ‘yan kasar Kenya da dama da ke yaki a Ukraine bayan da aka yi musu alkawarin za a biya su makudan kudade.