Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiKasafin 2026: Tinubu ya ware sama da tiriliyan 1 ga hukumar zabe...

Kasafin 2026: Tinubu ya ware sama da tiriliyan 1 ga hukumar zabe ta kasa

Gwamnatin Tinubu ta ware kudade ma su yawa a bangaren zabe

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ware Naira tiriliya 1.013 ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa, INEC, a cikin kasafin kuɗin 2026 da aka miƙa wa Majalisar Tarayya.

Bayanai sun nuna cewa wannan mataki na zuwa ne a matsayin shiri na musamman domin sharar fagen gudanar da zaɓen shekarar 2027.

Rahoton sun nuna cewa kudin da aka ware wa INEC na daga cikin kasafin kuɗin ƙasa baki ɗaya da ya kai N58.18tn, wanda gwamnatin Bola Tinubu ta amince da shi a bana.

A cikin cikakken bayani kan kasafin, gwamnatin tarayya ta kiyasta samun kuɗin shiga da yawansu ya kai N34.33tn, yayin da jimillar kuɗin da za a kashe suka kai N58.18tn.

Bayanai daga takardun kasafin kuɗin 2026 da Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya ya fitar sun nuna cewa adadin kuɗin da aka ware wa INEC ya kai N1,013,778,401,602.

An ce ware kuɗi ga hukumar INEC mai yawa a kasafin shekarar 2026 na nuna muhimmancin da gwamnati ke bai wa shirya zaɓe tun kafin lokaci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments