Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiƳan sanda sun yi nasarar kama gawurtattun ƴan bindiga biyu a Jihar...

Ƴan sanda sun yi nasarar kama gawurtattun ƴan bindiga biyu a Jihar Kwara

Rundunar yan sanda sun kama wasu sahararrun yan bindiga a Kwara

Jami’an sashen tattara bayanan sirri na rundunar ƴan sandan Najeriya, ta ce ta kama wasu riƙakkun ƴan bindiga biyu waɗanda ake zargi da kai munanan hare-hare a jihohin Katsina, Zamfara, Neja da kuma Kwara.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin ya fitar ranar Juma’a, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bayan wani samame da suka kai jihar Kwara.

A cewar sanarwar, an ga ɗaya daga cikin ƴan bindigar mai suna Abubakar Usman wanda aka fi sani da Siddi, yana wasa da maƙudan kuɗaɗe da kuma riƙe da makamai a wani bidiyo.

Ɗayan kuma an bayyana sunansa da Shehu Muhammadu wanda aka kuma sani da Gide.

Hundeyin ya ce jami’an sun ƙwato wata sabuwar mota ƙirar Hinda Ace, babura 125, bindigar AK-47 cike da tarin harsasai da kuma zunzurutun kuɗi da ya kai Naira 500,000.

“Bincike da muka fara gudanarwa ya nuna cewa waɗanda ake zargin mambobin wata gawurtacciyar ƙungiyar ƴan bindiga ne da ta ƙware wajen garkuwa da mutane a faɗin jihohin Zamfara da Katsina da Neja da kuma Kwara,”in ji sanarwar.

“Sun kuma kasance waɗanda ke samar da makamai da harsasai ga ɓata-gari.

“Dukkan waɗanda ake zargin na ci gaba da ba da haɗin-kai ga bincike don ganin an kai ga kama sauran mambobinsu da suke aikata ta’asar.

Mai magana da yawun ƴan sandan ya buƙaci al’umma da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai da suka kamata kan lokaci domin ganin an kawo karshen ayyukan ƴan bindiga.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments