Wednesday, November 11, 2026
HomeLabaraiA yau gwamna Abba Kabir zai gabatar da kasafin kudin 2027 ga...

A yau gwamna Abba Kabir zai gabatar da kasafin kudin 2027 ga majalisa

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen karɓar kudirin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf, a yau Laraba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce majalisar ta tabbatar da kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zaman gabatar da kasafin kuɗin, wanda gwamnan zai gabatar a gaban ’yan majalisar.

Sanarwar ta nuna cewa majalisar ta tanadi dukkan abubuwan da ake buƙata domin gudanar da zaman cikin tsari, inda ake sa ran gwamnan zai gabatar da bayanan kudirin kasafin kuɗin shekarar 2027.

Gabatar da kasafin kuɗin dai zai ba ’yan majalisar damar duba shirin kashe kuɗaɗen gwamnatin jihar a fannoni daban-daban, tare da gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu na majalisa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments