Wednesday, November 11, 2026
HomeKasuwanciGwamnatin tarayya ta ƙaddamar da aikin gina filin jirgin sama a Kogi

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da aikin gina filin jirgin sama a Kogi

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da aikin gina filin jirgin saman dakon kaya na ƙasa da ƙasa a Zariagi, ƙaramar hukumar Adavi ta jihar Kogi.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da aikin gina filin jirgin saman dakon kaya na ƙasa da ƙasa a Zariagi, ƙaramar hukumar Adavi ta jihar Kogi.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ne ya wakilci Tinubu wajen ƙaddamar da aikin ranar Talata, inda ya yaba wa Gwamna Ahmed Usman Ododo bisa ƙoƙarinsa na samar da ababen more rayuwa.

Keyamo ya ce filin jirgin zai jawo masu zuba jari tare da samar da ayyukan yi tsakanin 2,000 zuwa 3,000. Ya kuma bayyana cewa aikin zai ƙara wa jihar Kogi muhimmanci a harkokin sufurin jiragen sama na duniya.

Gwamna Ododo ya ce filin jirgin zai bunƙasa kasuwanci, sufuri, noma, haƙar ma’adinai da yawon buɗe ido, tare da sauƙaƙa wa manoma kai kayayyakin amfanin gonarsu kasuwannin cikin gida da na ƙasashen waje.

Kwamishinan Ayyuka, Momoh Salami Ozigi, ya ce matakin farko zai ƙunshi titin jirgin sama mai tsawon mita 3,600, wuraren ajiye jirage da sauran muhimman gine-gine. Ya ce kamfanin CCECC da ke aikin ya yi alƙawarin amfani da ƙwarewarsa wajen ganin an kammala aikin cikin nasara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments