Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce ta cire sunayen mutane 1,609,553 daga rajistar masu zaɓe, bayan gano cewa bayanansu ba su inganta ba.
INEC ta bayyana cewa daga cikin waɗanda aka cire, 1,608,660 bayanai ne marasa inganci, yayin da 873 suka kasance na mutanen da suka rasu.
Hukumar ta ce ta gano matsaloli da suka haɗa da rajista sau biyu, hotunan da aka samar da fasahar AI da kuma bayanan da ba su cika ba.
Sai dai INEC ta jaddada cewa mutane 1,545,052 da ke buƙatar ƙarin tantancewar yatsu ba a cire su kai tsaye daga rajistar ba.
Ta kuma ce ta gano wasu ma’aikata 54 a jihohi 10 da ake zargi da shigar da bayanan da ba su inganta ba, ciki har da hotunan AI. Hukumar ta ce za ta ɗauki matakin ladabtarwa da na shari’a a kansu.
Tsohon kwamishinan INEC, Festus Okoye, ya bukaci hukumar ta gudanar da sabon rajistar masu zaɓe bayan zaɓen 2027 tare da gurfanar da ma’aikatan da aka samu da laifi.