Jam’iyyar ADC ta shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ranar 5 ga Nuwamba, 2026, kan rikicin shugabancin jam’iyyar da ya shafi Nafiu Bala Gombe.
Haka kuma, jam’iyyar ta shigar da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an saurari ƙarar da ta shigar tare da yanke hukunci a kanta.
ADC ta ce ta sanar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) matakan da ta ɗauka a ranar 6 ga Nuwamba, tare da buƙatar hukumar da ta dakatar da duk wani mataki da ya shafi batun har sai kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci.
Daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC, Phrank Shaibu, ya ce bai kamata INEC ta yi watsi da ƙarar da buƙatar dakatar da hukuncin ba, domin hakan na iya kawo cikas ga tsarin shari’a.
Ya kuma buƙaci mambobi da magoya bayan jam’iyyar su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa ADC za ta ci gaba da yaƙin neman zaɓenta yayin da take amfani da duk hanyoyin da doka ta tanada wajen kare haƙƙinta.
Shaibu ya jaddada cewa jam’iyyar na da yakinin za a saurari hujjojinta da kuma dokokin da suka shafi shari’ar, tare da bai wa dukkan ɓangarori damar samun adalci.