Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi da laifuffuka (UNODC) ta buƙaci a bai wa matasa damar shiga harkokin tsara manufofi da zaɓe a Najeriya.
An bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru biyar na shirin Nigeria Youth Futures Fund (NYFF), wanda aka gudanar a Abuja.
Shugabar LEAP Africa, Kehinde Ayeni, ta bukaci gwamnatoci su riƙa sabunta manufofin matasa, tare da samar musu da horo da damar shiga wuraren yanke shawara.
Ta ce shirin ya taimaka wa matasa sama da 22,000, tare da tallafa wa ƙungiyoyi sama da 1,000 da matasa ke jagoranta a sassan Najeriya.
Wakilin UNODC a Najeriya, Cheikh Ousmane Toure, ya ce bai kamata a bar matasa a gefe ba, musamman yayin da ake tunkarar zaɓukan da ke tafe, yana mai cewa ra’ayoyinsu na da muhimmanci wajen gina makomar ƙasar.