Sojin Najeriya ta kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne guda biyu, tare da kuɓutar da wani mutum da aka sace, sannan ta ƙwato kuɗin fansa naira miliyan 10 a dajin Falgore, da ke ƙaramar hukumar Doguwa a jihar Kano.
Aikin ya gudana ne ƙarƙashin rundunar sojojin Brigade ta 3, a wani samame na Operation MESA, bayan sace Alhaji Kabiru Aliyu a ƙauyen Fanyabo da ke cikin dajin a ranar 11 ga Oktoba, 2026.
A cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Babatunde Zubairu, ya fitar ranar Asabar, ya ce an sace Kabiru ne da tsakar dare yayin da yake dawowa daga kasuwar Yandoka da ke jihar Kaduna.
Sanarwar ta ce bayan sace shi, masu garkuwar sun tuntubi iyalansa da ke ƙauyen Yan Taburmi, inda suka buƙaci a biya kuɗin fansa domin sakin sa. Daga bisani, sojoji sun samu sahihan bayanan sirri, suka yi kwanton ɓauna tare da haɗin gwiwar ’yan sanda, DSS da mafarautan yankin.
A yayin samamen, sojojin sun kashe mutum biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, suka kuɓutar da wanda aka sace, yayin da sauran waɗanda ake zargin suna cikin ƙungiyar suka tsere zuwa cikin dajin Falgore.
Bayan binciken yankin, sojojin sun gano tare da ƙwato naira miliyan 10 da aka ce iyalan wanda aka sace sun biya a matsayin kuɗin fansa. An mayar da kuɗin ga mutumin da iyalansa.
Kwamandan rundunar Brigade ta 3, Birgediya Janar Saka Jimoh, ya yaba wa sojojin bisa ƙwarewa da jajircewarsu, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka domin kare tsaro a Kano.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su riƙa ba hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.