Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasa2027: Peter Obi ya rasa damar lashe zaɓe tunda ya fice daga...

2027: Peter Obi ya rasa damar lashe zaɓe tunda ya fice daga ADC – Tsohon gwamnan Ekiti

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce Peter Obi ya rage wa kansa damar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027 tun bayan ficewarsa daga jam’iyyar ADC zuwa NDC.

Fayose ya bayyana hakan ne yayin wata hira da TVC News, inda ya ce rashin haɗin kan jam’iyyun adawa na iya ƙara wahalar da Obi wajen samun nasara a zaɓen 2027.

A cewarsa, rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan adawa na iya zama babban kalubale ga duk wani ɗan takarar da ke son kalubalantar jam’iyyar APC a zaɓen mai zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments