Monday, October 19, 2026
HomeLabarai’Yan sandan jihar Delta sun ceto matar da aka yi fataucin ta...

’Yan sandan jihar Delta sun ceto matar da aka yi fataucin ta zuwa Côte d’Ivoire

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta ceto wata ’yar Najeriya mai shekaru 25 da aka yi fataucin ta zuwa ƙasar Côte d’Ivoire, tare da kama wata mata mai suna Ese Betty Isiorho, mai shekaru 26, bisa zargin yaudarar mata da safarar su zuwa ƙasashen waje domin tilasta musu yin karuwanci.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta ceto wata ’yar Najeriya mai shekaru 25 da aka yi fataucin ta zuwa ƙasar Côte d’Ivoire, tare da kama wata mata mai suna Ese Betty Isiorho, mai shekaru 26, bisa zargin yaudarar mata da safarar su zuwa ƙasashen waje domin tilasta musu yin karuwanci.

Mai magana da yawun rundunar, SP Bright Edafe, ya ce bincike ya nuna cewa wadda ake zargin ta yaudari matar ne da alkawarin koyon sana’ar gyaran gashi a Côte d’Ivoire. Sai dai bayan isarta ƙasar, an tilasta mata shiga harkar karuwanci maimakon aikin da aka yi mata alkawari.

‘Yan sanda sun ce wadda ake zargin ta amsa cewa ta kai mata biyu zuwa Côte d’Ivoire, inda aka miƙa su ga wata da aka fi sani da Madam Purity, wadda ake zargi da tilasta musu yin karuwanci. Daga bisani jami’an tsaro suka samu nasarar ceto ɗaya daga cikin matan tare da dawo da ita Najeriya.

An bayyana cewa matar da aka ceto ta haɗu da iyalanta kuma tana samun kulawar da ta dace, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto ɗaya matar da har yanzu ke hannun masu safarar mutane a Côte d’Ivoire.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Delta, CP Yemi Oyeniyi, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da fataucin mutane da sauran manyan laifuka. Ya kuma gargadi jama’a da su yi taka-tsantsan da tayin ayyuka ko koyon sana’o’in bogi a ƙasashen waje.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments