Fitaccen lauya kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam a Najeriya, Femi Falana (SAN), ya yi barazanar gurfanar da gwamnatin tarayya a gaban kotu kan gina wa manyan alƙalan ƙasar gidajen alfarma a Abuja.
Falana ya bayyana cewa, a fahimtarsa, babu wata doka da ta bai wa gwamnati damar aiwatar da irin wannan tsari, yana mai cewa matakin ya saɓa da ƙa’idojin doka.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da batun rabon gidajen ke ci gaba da janyo muhawara da martani daga sassa daban-daban na ƙasar.