Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTinubu ya bukaci shugabanni su yi koyi da kyawawan dabi’un marigayi Buhari

Tinubu ya bukaci shugabanni su yi koyi da kyawawan dabi’un marigayi Buhari

Tinubu ya bayyana cewa rayuwar Buhari ta kasance abin koyi wajen hidimtawa ƙasa, riƙon amana, gaskiya da kuma kishin ƙasa.

Ya ce waɗannan dabi’u ne da ya kamata shugabanni su ci gaba da runguma domin inganta shugabanci a ƙasar.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga shugabannin Najeriya da su ci gaba da gudanar da mulki bisa kyawawan dabi’u da manufofin marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya wakilci Shugaba Tinubu a wajen taron addu’o’in cika shekara guda da rasuwar Buhari, wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja ranar Litinin.

A cewarsa, marigayi Buhari ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Najeriya hidima, kuma irin gudunmawar da ya bayar za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa ga al’umma da masu rike da madafun iko.

Shugaban ya jaddada cewa ci gaba da bin tafarkin gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa da Buhari ya tsaya a kai zai taimaka wajen gina Najeriya mai ɗorewa da ci gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments