Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSiyasa da wariyar jinsi sun hana mata ci gaba a ɓangaren shari'ar...

Siyasa da wariyar jinsi sun hana mata ci gaba a ɓangaren shari’ar a Sokoto – FIDA

Ƙungiyar Lauyoyin Mata ta Duniya (FIDA) reshen Jihar Sokoto ta bayyana cewa tsoma bakin siyasa, wariyar jinsi da al’adu na daga cikin manyan matsalolin da ke hana mata samun aiki, ƙarin girma da kuma mukaman jagoranci a bangaren shari’ar jihar.

Ƙungiyar Lauyoyin Mata ta Duniya (FIDA) reshen Jihar Sokoto ta bayyana cewa tsoma bakin siyasa, wariyar jinsi da al’adu na daga cikin manyan matsalolin da ke hana mata samun aiki, ƙarin girma da kuma mukaman jagoranci a bangaren shari’ar jihar.

An bayyana hakan ne a wani taron horaswa da aka shirya wa alkalai mata da ma’aikatan shari’a, inda FIDA ta gabatar da sakamakon binciken da ta gudanar kan ƙalubalen da mata ke fuskanta a fannin shari’a a jihar.

Binciken ya nuna cewa duk da ƙarin yawan mata da ke shiga harkar shari’a, har yanzu suna fuskantar matsaloli na tsarin aiki, al’adu da addini, waɗanda ke hana su samun damar ci gaba daidai da maza.

FIDA ta ce tsoma bakin siyasa, son kai da amfani da alaƙa wajen ɗaukar ma’aikata da ba su muƙamai na sa ba koyaushe ake yin hakan bisa cancanta da ƙwarewa ba, lamarin da ke rage amincewa da tsarin.

Rahoton ya kuma nuna cewa matan da suka auri ’yan asalin Sokoto amma ba su fito daga jihar ba kan fuskanci wariya wajen ɗaukar aiki da ƙarin girma, saboda fifita asalin jihar fiye da cancanta. Haka kuma, wasu mata sun koka da cin zarafi a wurin aiki, ƙarancin tallafi ga waɗanda ke aiki a yankunan karkara, da kuma rashin shirye-shiryen jagoranci da kariya ga mata. FIDA ta buƙaci a samar da manufofi masu kare haƙƙin mata, ƙarfafa ’yancin bangaren shari’a da kuma inganta shirye-shiryen da za su bai wa mata damar kai wa manyan muƙamai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments