Sunday, October 18, 2026
HomeTsaro’Yan bindiga sun kashe fitaccen ɗan kasuwa bayan karɓar kuɗin fansa a...

’Yan bindiga sun kashe fitaccen ɗan kasuwa bayan karɓar kuɗin fansa a Katsina

An shiga alhini da jimami a Jihar Katsina bayan rahotanni sun tabbatar da cewa wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe fitaccen ɗan kasuwa kuma manomi, Bala Sanin Kawo, bayan sun yi garkuwa da shi a Ƙaramar Hukumar Dandume ta jihar.

Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa an sace Bala Sanin Kawo tare da ɗaya daga cikin ma’aikatansa a ranar Alhamis yayin da suke dawowa daga gonarsa da ke kusa da ƙauyen Dantakari.

Bayan sace su, masu garkuwar sun tuntubi iyalansa tare da neman kuɗin fansa domin su sake shi.

Sai dai duk da ƙoƙarin da aka yi na ganin an kuɓutar da shi, daga bisani aka samu labarin cewa an kashe shi.

Mutuwar Bala Sanin Kawo ta girgiza al’ummar yankin Dandume da ma jihar baki ɗaya, inda mutane da dama suka bayyana alhininsu kan yadda matsalar garkuwa da mutane da hare-haren ’yan bindiga ke ci gaba da salwantar da rayuka da dukiyoyi.

Lamarin ya sake tayar da hankalin jama’a kan matsalar rashin tsaro da ke addabar wasu sassan Jihar Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yamma, inda ake ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments