Wata mummunar gobara da ta lalata ginin kotun Floyd County a Amurka ta tilasta rufe kotuna tare da kawo cikas ga ayyukan gwamnati a duk faɗin yankin.
Jami’ai sun ayyana dokar ta-baci a harkar shari’a bayan gobarar ta tashi a ginin kotun da ke kan West Fifth Avenue, lamarin da ya hana shiga cikin ginin tare da haifar da fargabar tsaro.
An fara samun rahoton gobarar ne dai a ranar Litinin, inda aka fitar da dukkan ma’aikatan da ke cikin ginin nan take, kamar yadda jami’an yankin suka bayyana.
Wasu bayanai da hukumomi suka fitar sun tabbatar da cewa ba a samu rahoton jikkata ko rauni ba ga ko mutum daya da ke cikin ginin.
‘Yan kashe gobara sun kai dauki Jami’an kashe gobara sun shafe sa’o’i suna kokarin shawo kan gobarar yayin da hayaki ya bazu a tsakiyar birnin Rome.
A lokacin da ake kokarin kashe wutar, hukumomin tsaro sun rufe hanyoyin da ke kusa yayin da ake gudanar da aikin ceto wadanda ke cikin ginin.