Sunday, October 18, 2026
HomeKasashen wajeRikici ya sake ɓarkewa tsakanin Pakistan da Afghanistan

Rikici ya sake ɓarkewa tsakanin Pakistan da Afghanistan

Pakistan ta bayyana shirin shiga yaƙi da Afghanistan bayan ruwan bama-baman da ta yi da jiragen yaƙi a tsakar birnin Kabul a wani yanayi da kuma ake ci gaba da fafatawa a kan iyakar ƙasashen biyu.

Cikin wata sanarwa da ministan tsaron Pakistan Khawaja Asif ya fitar ta bayyana cewa kai tsaye sun shiga yaƙi da maƙwabciyar tasu.

Ƙasashen biyu dukkaninsu masu rinjayen musulmi sun jima suna takun saƙa da juna wanda ya tsananta tun bayan zuwan Firaminista Shehbaz Sharif karagar mulki.

Tun farko Pakistan ta fara kai hare-hare a garuruwan kan iyaka a tsakaninta da Afghanistan a ƙarshen makon wanda ta ce ta kai harin ne da nufin farautar ƴan ta’addan TTP da ke samun mafaka a makwabciyartata sai dai harin ya rutsa mutane fiye da 80 ƴan Afghanistan, lamarin da ya sanya Kabul shan alwashin mayar da martani.

A jiya ne dai aka fara musayar wuta akan iyakar ƙasashen biyu bayan hare-haren da Afghanistan ta kai wanda Pakistan ta mayar da martani ta hanyar luguden wuta a birnin Kabul.

Mazauna yankunan kan iyaka na cike da fargaba sakamakon yadda ake ci gaba da musayar wuta.

Dukkanin ƙasashen biyu sun sanar da kashe musu ɗimbin mutane cikin ƴan kwanaki da faro wannan rikici.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments