Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAES ta ƙaddamar da rundunar da zata rika ba wa kasashen Nijar,...

AES ta ƙaddamar da rundunar da zata rika ba wa kasashen Nijar, Mali, Burkina Faso tsaro

AES ta kafa sabuwar rundunar da za ta yi aiki wajen kare duk wata barazanar tsaro

Haɗakar AES ta ƙaddamar da rundunarta da za ta yi aikin samar da tsaro tsakanin ƙasashen 3 na Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, rundunar da aka ƙaddamar a birnin Bamako ƙarƙashin jagorancin Janar Assimi Goita.

Samar da rundunar ƙawancen mai ɗauke da dakaru 5,000, shi ne yunƙuri na baya-bayan nan da ƙasashen ke yi don tabbatar da tsaro da zaman lafiyarsu daidai lokacin da suke ganin barazanar mayaƙan ta’addanci da ke iƙirarin jihadi.

Ƙawancen na AES ya ce wannan runduna za ta yi aiki wajen kange duk wata barazana da ke tunƙaro ƙasashen na Sahel uku.

Tun a watan Janairun shekarar nan, ministan tsaron Jamhuriyyar Nijar ya yi shelar samar da wannan runduna mai ɗauke da dakaru 5,000 don yaƙar matsalolin tsaron ƙasashen 3 sai dai a yanzu ne aka iya ƙaddamar da wannan runduna.

Yayin ƙaddamar da wannan runduna an naɗa Janar Daouda Traore na Burkina Faso a matsayin wanda zai jagoranceta yayin da babban sansaninta zai ci gaba da kasancewa a birnin Niamey fadar gwamnatin Nijar.

Bikin ƙaddamar da rundunar ya samu halartar ministocin tsaron ƙasashen 3 da jakadun ƙasashen na AES da sauran wakilcinsu a hukumomin duniya.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments