Dakarun rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), da haɗin gwiwar ƴan sintirin sa kai sun kashe mayaƙan ISWAP 17 a wani samame da suka kai da sanyi safiyar Lahadi, 21 ga watan Disamban 2025.
Kakakin rundunar, Laftanal kanal Sani Uba, ya ce sun yi nasarar ne bayan tattara bayanan sirri a kan zirga-zirgar mayaƙan.
Ya ce dakarun sun ”tarwatsa maɓoyar ƴan ta’addan ƙungiyar JAS da na ISWAP a ƙauyukan Sojiri da Kayamla na jihar Borno.”
“Da misalin ƙarfe 2:24 na dare mayaƙan suka taru kan babura a wani waje da suke karɓar kayyakin da ake masu safara, lamarin da ya tabbatar da rahoton sirri da muke da shi.”
“Daga nan sai dakarunmu da suke ɓoye suka buɗe masu wuta kuma suka kashe da dama a cikin su,” in ji Laftanal Kanal Uba.
Ya bayyana cewa a yayin arangamar, dakarun sun kashe mayaƙan 17 kuma wasu da dama sun gudu da munanan raunuka a jikinsu.
Daga cikin kayan da aka ƙwato daga hannun mayaƙan akwai babura da kayan abinci da magunguna da kayan sawa da kuma bindigu da alburusai kala-kala.