Tuni aka fara cin karo da direbobin da ke harkar kwaya, bayan gwajin da aka yi da ya bankado su, lamarin da ya daga hankalin fasinjoji.
Wannan dai shine karon farko da aka fara irin wannan gwajin kan direbobi, wanda gwamnati ta ce yawaitar haɗurran da ake samu na da nasaba ne da shan ƙwaya da direbobi ke yi.
Kamar yadda bayanai suka nuna, daga shekarar 2020 zuwa 2024, an yi hadari 59,000 da ya lakume rayuka 5,000.