Mazauna garin Spin Boldak na Afghanistan sun tsere daga gidajensu, wanda ke kan iyakar ƙasashen mai tsawon kilomita 2,600.
Wani ma’aikacin lafiya a garin Kandahar ya bayyana cewa an kai gawar mutum huɗu asibitin yankin tare da raunata wasu mutum huɗu.
An kuma raunata wasu mutum uku a Pakistan.
Ƙasashen biyu dai sun yi ta gwabzawa a ‘yan watannin nan, yayin da Taliban ke zargin Pakistan da kai hare-hare ta sama cikin Afghanistan.
Ɓangarorin biyu sun tabbatar da fafatwar a cikin dare amma sun zargi juna da fara kai harin da ya jawo ɓarin wuta na kusan awa huɗu.