Rahotanni sun bayyana cewa mutum uku sun mutu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon sabon rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin Paikon-Kore, da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada, a Babban Birnin Tarayya (FCT).
Haka kuma, an kona gidaje da babur, tare da lalata kayayyaki da dama a shagunan da ke kasuwar garin.
Rikicin, wanda ya fara da yammacin ranar Asabar, ya ci gaba har zuwa safiyar Lahadi, inda shaguna da dama a kasuwar garin Paikon-Kore suka ƙone, tare da lalata kayayyakin da ke cikinsu.
Masana sun yi kira da a gaggauta ɗaukar matakan shawo kan rikicin tun kafin ya ƙazanta, domin kauce wa maimaita irin munanan rikice-rikicen da aka sha gani a jihohin Benue da Filato, inda rikicin manoma da makiyaya ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da raba da dama da muhallansu.
Wani mazaunin yankin, Danlami Ibrahim, ya ce rikicin ya fara ne bayan wasu makiyaya sun bar shanunsu suka shiga gonar gyada da ba a girbe amfanin cikinta ba.
Ya ce mai gonar ya tunkari makiyayan domin nuna rashin jin daɗinsa kan shigar shanun gonarsa, lamarin da ya haifar da sa-in-sa tsakaninsu.
A cewarsa, ɗaya daga cikin makiyayan ya zaro adda tare da kai wa wani manomi hari, inda ya sare masa hannu.
Ibrahim ya bayyana cewa lamarin ya fusata mazauna yankin, musamman bayan labarin raunin da manomin ya samu ya bazu ga sauran mutanen gari. Hakan ya haifar da ramuwar gayya, inda aka ruwaito an kashe makiyaya uku.
Sakataren ƙungiyar makiyayan shanu ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), reshen ƙaramar hukumar Gwagwalada, Mohammed Usman, ya tabbatar da mutuwar makiyaya uku.
“Ya zuwa yanzu, bayanan da nake da su sun nuna cewa makiyaya uku sun rasa rayukansu. Wannan shi ne abin da zan iya cewa a yanzu, domin har yanzu ban samu adadin waɗanda suka jikkata ba,” in ji shi.
Usman ya ce zai fitar da ƙarin bayani idan ya samu, inda ya ƙara da cewa ya sanar da shugaban ƙaramar hukumar Gwagwalada, Kasim Mohammed Ikwa, game da lamarin.
Zuwa yanzu, rundunar yan sandan Abuja ba ta ce komai game da rikicin ba.