Rundunar ’yan sandan Jihar Delta da ke kudancin Najeriya ta ce ta kama mutum 67 da ake zargin mambobin ƙungiyar asiri ta Supreme Vikings Confraternity ne yayin bikin cikar ƙungiyar shekara a Asaba, babban birnin jihar.
Mai magana da yawun rundunar, Bright Edafe, ya bayyana cewa waɗanda aka kama sun haɗa da maza 55 da mata 12. Ya ce an kama su ne bayan jami’an tsaro sun samu bayanan sirri cewa sun taru a wani otal da ke kan hanyar Abraka a Asaba.
A yayin samamen, jami’an tsaro sun ƙwato bindigogin harba harsasai masu yawa guda biyu, bindiga guda da aka ƙera a gida, harsasai masu rai guda 10 da wasu kayayyakin da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan ƙungiyar asiri.
A wani samame na daban, ’yan sanda sun kama wasu mutum 15 da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar a garin Agbor, yayin da aka kama wasu mutum uku a wani wurin da ake zargin mafakar masu aikata laifuka ce a al’ummar Jeremy, da ke ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu.
Haka kuma, an kama wasu maza 10 a Jeddo, da ke ƙaramar hukumar Okpe, bisa zargin aikata ayyukan ƙungiyar asiri.
Rundunar ta ce a jimlace ta ƙwato bindigogi guda biyar, harsasai masu rai guda 12 da kuma harsasai guda bakwai da aka riga aka harba daga samamen.
Ta ƙara da cewa tana tsare da waɗanda ake zargin tare da kayayyakin da aka ƙwato, yayin da ake ci gaba da bincike.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Samuel Erale, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da samamen, tare da umartar su da ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ƙungiyoyin asiri.
Ya kuma gargaɗi cewa rundunar ba za ta lamunci ayyukan da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma ba, inda ya buƙaci mazauna jihar su riƙa kai wa ’yan sanda sahihan bayanai.