Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSojoji kaɗai ba za su iyamagance matsalar ’yan bindiga a Sokoto ba...

Sojoji kaɗai ba za su iyamagance matsalar ’yan bindiga a Sokoto ba – Ribadu

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana muhimman matakai biyar da ya ce ya kamata a ɗauka domin shawo kan matsalar ’yan bindiga a Jihar Sokoto, yana mai cewa aikin soji kaɗai ba zai iya kawo ƙarshen matsalar ba.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa daraktan harkokin shari’a a ofishin Ribadu, Zakari Mijinyawa, ne ya bayyana hakan a madadinsa, yayin wani taron tattaunawa kan tsaro da aka gudanar a Sokoto.

Matakan sun haɗa da ƙarfafa musayar bayanan sirri tsakanin jami’an tsaro, tsaurara tsaron iyakoki, inganta haɗin gwiwa tsakanin al’umma da jami’an tsaro, kare harkokin noma da tattalin arzikin karkara, da kuma hana matasa shiga ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Ribadu ya bayyana cewa ayyukan ’yan bindiga sun wuce satar shanu da garkuwa da mutane, inda a yanzu suke ƙwace ikon wasu yankuna, karɓar haraji ba bisa ƙa’ida ba da kuma kawo cikas ga harkokin tattalin arziki.

Ya kuma nuna cewa kusancin Jihar Sokoto da Jamhuriyar Nijar da yankin Sahel na ƙara sauƙaƙa zirga-zirgar ƙungiyoyin masu aikata laifuka ta kan iyakoki.

Saboda haka, ya buƙaci ƙarfafa tsarin gargaɗin farko a ƙananan hukumomin Sabon Birni, Isa, Tangaza da Goronyo, tare da tabbatar da cewa ana auna nasarar yaƙi da ta’addanci ta hanyar dawo da zaman lafiya, sake buɗe makarantu da kasuwanni, da kuma ba manoma damar komawa gonakinsu.

A cewarsa, haɗa matakan tsaro da na tattalin arziki da haɗin kan al’umma na da muhimmanci wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments