Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaRikicin cikin gida na APC ya fi ba ni damuwa fiye da...

Rikicin cikin gida na APC ya fi ba ni damuwa fiye da Atiku da Obi – Shettima

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa saɓani da rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar APC sun fi ba shi damuwa fiye da ’yan adawa, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi, gabanin zaɓen shekarar 2027.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Shettima ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Abuja, yayin ƙaddamar da babban ofishin yaƙin neman zaɓen ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A), wadda ke goyon bayan tikitin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shi kansa.

Shettima ya ce bai fi tsoron ’yan adawa ba, sai dai rashin haɗin kai a cikin jam’iyyarsu. Ya jaddada cewa idan ’yan APC suka haɗa kai, za su samu damar fafatawa a zaɓen mai zuwa.

Ya kuma gargaɗi shugabannin Arewa da kada su nemi nasarar zaɓen shugaban ƙasa ta hanyar raunana gwamnonin jam’iyyarsu a zaɓen jihohi, yana mai cewa ya kamata su tallafa wa juna domin samun nasara a dukkan matakan zaɓe.

Mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci ’yan APC su goyi bayan gwamnoninsu, ’yan majalisun tarayya da Shugaba Tinubu, tare da neman amincewar ’yan Najeriya cikin tawali’u gabanin babban zaɓen 2027.

Dangane da Atiku Abubakar, Shettima ya bukaci mambobin APC da su fafata da shi cikin mutunci, yana mai cewa jam’iyyar tana da tsarin da zai ba ta damar fafatawa a kowace rumfar zaɓe.

Haka kuma, Shettima ya kare nasarorin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, inda ya bayyana cewa ajiyar kuɗin waje ta Najeriya ta kai dala biliyan 58.9.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments