Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta kafa kwamitin yaƙi da satar fitilun ‘solar’ a kan...

Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin yaƙi da satar fitilun ‘solar’ a kan tituna

Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kwamiti na musamman domin ɗaukar mataki kan masu satar fitilun solar da aka girka a kan tituna, a ƙoƙarin kare kayayyakin more rayuwar jama’a.

Siyasarmu TV ta ruwaito cewa Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Injiniya Marwan Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi da gidan rediyon Kano.

Kwamishinan ya ce abin takaici ne yadda wasu bata gari ke fakewa da dare domin sace fitilun solar da aka sanya a kan tituna, duk da kuɗaɗen da gwamnati ta kashe wajen samar da su.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki matakan da suka dace domin dakile wannan ɗabi’a tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a satar kayayyakin more rayuwar jama’a.

Matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na kare kayayyakin more rayuwa da tabbatar da cewa jama’a sun amfana da ayyukan da aka samar domin inganta rayuwarsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments