Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiLabaraiA rana irin ta yau aka haifi fitaccen mai fafutuka, Mahatma Gandhi

A rana irin ta yau aka haifi fitaccen mai fafutuka, Mahatma Gandhi

Gandhi ya koya wa duniya muhimmancin amfani da lalama da tattauna wa wajen neman yanci maimakon tashin hankali da amfani da makamai

Mahatma Gandhi, wanda ainihin sunansa Mohandas Karamchand Gandhi, yana ɗaya daga cikin fitattun shugabannin duniya da suka yi fice wajen gwagwarmayar neman ’yanci ta hanyar zaman lafiya. An haife shi a rana irin ta yau, 2 ga Oktoba, 1869, a Porbandar, jihar Gujarat ta Indiya. Ya karanci aikin lauya a Landan, inda ya kammala karatunsa a shekarar 1891.

A shekarar 1893, Gandhi ya tafi Afirka ta Kudu, inda ya fuskanci wariyar launin fata. Wannan ya sa ya fara fafutukar kare haƙƙin al’umma, tare da ƙirƙirar dabarar Satyagraha, wato gwagwarmaya ta hanyar gaskiya da zaman lafiya ba tare da makami ba.

Gandhi ya koma Indiya a shekarar 1915, inda ya jagoranci gwagwarmayar neman ’yancin kai daga Birtaniya. Daga cikin manyan fafutukarsa akwai Tattakin Gishiri na 1930 da Quit India Movement na 1942. Daga bisani, Indiya ta samu ’yancin kai a ranar 15 ga Agusta, 1947.

A ranar 30 ga Janairu, 1948, Nathuram Godse ya harbe Gandhi har lahira a New Delhi. Duk da mutuwarsa, Gandhi ya bar babban tarihi, musamman ta hanyar koyarwar zaman lafiya da rashin amfani da ƙarfi wajen neman ’yanci. Dabarunsa sun yi tasiri ga shugabanni irin su Martin Luther King Jr. da Nelson Mandela.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments