Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiMDD, ICRC sun yi gargadi kan amfani da makamai masu sarrafa kansa

MDD, ICRC sun yi gargadi kan amfani da makamai masu sarrafa kansa

Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, da shugabar Ƙungiyar Agaji ta ICRC, Mirjana Spoljaric, sun yi gargaɗi kan shirin wasu ƙasashe na amfani da makamai masu sarrafa kansu wajen kai hare-hare.

A wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, shugabannin biyu sun ce abin damuwa ne yadda ake shirin amfani da waɗannan makamai wajen kashe dimbin mutane ba tare da cikakken sa hannun mutum ba.

Sun kuma yi kira da a gudanar da tattaunawa tsakanin ƙasashe domin samar da ƙa’idoji da za su takaita amfani da irin waɗannan makamai tare da kare rayukan fararen hula.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments