Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTinubu ya ba da umarnin kama wanda ake zargi da kafa hukumar...

Tinubu ya ba da umarnin kama wanda ake zargi da kafa hukumar bogi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin a gaggauta kama Yarima George Buchi Nwabueze, bisa zargin alakarsa da kafa wata hukumar da ake zargin ba ta da tushe.

Hukumar da ake magana a kai na dauke da sunan National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office, wadda aka gano a cikin ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), Dr. Musa Adamu Aliyu, SAN, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai na fadar shugaban kasa bayani bayan ganawarsa da Shugaba Tinubu a ranar Juma’a.

Ya ce ICPC ce ta gano batun, lamarin da ya sa Shugaban Kasa ya bayar da umarnin a dauki matakin gaggawa kan wanda ake zargin yana da hannu a kafa hukumar.

Ana sa ran jami’an tsaro za su ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kan yadda aka kafa hukumar da kuma mutanen da ke da hannu a lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments